Sunday 8 February 2026 - 22:30
Gargadin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Game da Danganta Alamomin Bayyanar Imam Mahdi (A.S)!

Hauza/ Abin takaici, daya daga cikin manyan kalubale a kan batun Mahdawiyya shi ne rarraba ra’ayoyin jahilci da kuma danganta alamomin bayyanar Imam Mahdi (A.S) da abubuwan da ba su da tabbataccen dalili. Wannan wata karkatacciyar hanya ce wadda a tsawon tarihi ta share fage ga masu ikirarin karya, sannan ta mayar da asalin gaskiyar jiran Imam Mahdi (Intizar) baya.

A cewar Ofishin Yada Labaran Hauza, ga kadan daga cikin bayanan Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci (Ayatullah Khamenei) game da batun danganta alamomin bayyanar Imam Mahdi, wadanda ya bayyana a gaban masana fannin Mahdawiyya:

Shin ya dace a danganta alamomin bayyanar Imam Mahdi?

Daya daga cikin manyan hadari a kan batun Mahdawiyya shi ne ayyukan jahilci, wadanda ba su da asali, kuma suka dogara akan tunanin banza da rudu. Wannan yana share fage ga masu ikirarin karya kuma yana janye mutane daga hakikanin gaskiyar jiran Imam Mahdi.

A tsawon tarihi, an samu wasu mutane da suka danganta wasu alamomin bayyanar Imam Mahdi ga kansu ko ga wasu mutane; dukkan wadannan abubuwa kuskure ne kuma barna ne. Domin wasu daga cikin bayanan da suka shafi alamomin bayyanar Imam ba su da tushe mai karfi, kuma koda ingantattun bayanan ma, ba za a iya danganta su da mutane ko lokuta cikin sauki ba.

Irin wadannan bayanan karya kuma karkatattu suna sa ainihin gaskiyar Mahdawiyya da jiran Imam su zama abin wulakantarwa ko boyewa. Saboda haka, dole ne a kiyaye tare da nisantar jita-jita da ayyukan jahilci na gama-gari. (09/07/2011)

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha